Daga John D.Wada, a Lafiya
Hukumar kiwon lafiya ta matakin farko ta gwamnatin jihar Nasarawa tace a yanzu haka tana aiki tukiru ne tare da haɗin gwiwar babban bankin duniya da sauran abokan hulɗa wajen inganta harkokin ta na kiwon lafiya a fadin jihar baki daya.
Shugaban hukumar Dokts Usman Iskilu Saleh ne ya sanar da hakan a lokacin da yake karɓar baƙuncin ƙungiyar masu aiko da rahotanni wato correspondents chapel a turance ta kasa reshin jihar ta Nasarawa a hukumar dake Lafiya babban birnin jihar a mako da ake ciki.
Yace a yanzu haka hukumar tasa tana yin haka ne musamman ta sabunta duka asibitocin jeka da gidan ka sama da 50 dake jihar wadanda acewar sa hakan yana kuma taimaka wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga jama’a tare da rage kuɗin da suke kashewa wajen Neman lafiya da sauran su.
Dokta Usman Iskilu Saley ya ƙuma bayyana cewa ana sa ran kammala aikin kafin karsshen watan Yuni, sannan an shirya tabbatar da cewa dukkanin gundumomi 147 na jihar suna da asibiti ɗaya da ke aiki dare da rana
Ya jinjina wa gwamnan jihae Injiniya Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya a jihar baki daya kawo yanzu tunda ya karagar Mulki.
Bugu da kari shugaban na hukumar kiwon lafiya na matakin farko a jihar ta Nasarawa dokta Usman Iskilu Saleh ya buƙaci a samu haɗin gwiwa da hukumonin isar da labarai dabandaban a jihar dama qasa baki daya da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da zuwa asibiti don bincike da magani.
Tunfarko a jawabin shugaban qungiyar masu aiko da rahotanni ta qasa reshin jihar Nasarawa mista Isaak Ibgju yace ‘yan jaridar sun kasance a sakatariyar Hukumar ne don taya sabon shugaban murnar nadin sa tare da tabbatar masa cewa a shirye suke su cigaba da aiki tare da Hukumar don samun cigaba musamman a fannin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar baki daya.